logo

HAUSA

Sin na cikin kasashe mafiya tsaro a duniya

2024-04-15 20:36:47 CMG Hausa

Yau Litinin 15 ga watan nan na Afrilu, rana ce ta fadakar da daukacin al’umma kan tsaron kasa karo na 9 a kasar Sin, inda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Lin Jian, ya bayyana cewa, shekarar da muke ciki, ita ce ta cika shekaru goma tun bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bullo da ra’ayin tabbatar da tsaron kasa daga dukkan fannoni, wanda a karkashinsa, kasar ta cimma dimbin nasarori ta fuskar kiyaye tsaron kasa a sabon zamanin da muke ciki, kana kuma an kiyaye cikakken yankin kasa, da tsaro, gami da moriyar ci gaba daga dukkanin fannoni, da tabbatar da zaman rayuwar al’umma yadda ya kamata, matakin da ya sa kasar ta zama daya daga cikin kasashe mafiya tsaro a dukkan fadin duniya.

Kakakin ya jaddada a wajen taron manema labaran da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta shirya a yau Litinin cewa, kasarsa za ta ci gaba da gudanar da harkokin diflomasiyyarta daidai, bisa ra’ayin tabbatar da tsaron kasa daga dukkanin fannoni, da kiyaye tsaron duk duniya, yayin da take kokarin kiyaye tsaron gida, da aiwatar da shawarar kiyaye tsaro a duk duniya, don hada kan kasashe daban-daban, wajen shawo kan kalubalolin tsaro iri-iri, da raya duniya mai dauwamammen zaman lafiya da cikakken tsaro. (Murtala Zhang)