logo

HAUSA

Kasar Sin ta kammala wani zagaye na gwajin injin din rokar mai da za a iya sake amfani da shi

2024-04-15 10:13:41 CMG Hausa

A cikin ’yan shekarun nan, kasar Sin ta ci gaba da bunkasa fasahohin ababen jigila na sararin samaniya, kuma sabuwar nasarar da aka samu ita ce nasarar gwajin kunna injin mai daukar tan 130 na iskar oxygen da kananzir wanda zai kunna rokar dakon kaya da ake iya sake amfani da shi.

Injin din da ake sake amfani da shi wanda wata cibiyar da ke karkashin babban kamfanin kimiyya da fasahar sararin samaniya ta kasar Sin ta kera, an kunna shi sau biyu a ranar Juma’a a wurin gwajin dake lardin Shaanxi a arewa maso yammacin kasar.

Ya zuwa yanzu ya kammala jimillar gwaje-gwaje 15 da aka maimaita da kunnawa sau 30, tare da jimillar lokacin gwajin da ya wuce dakika 3,900. Yawan gwaje-gwajen da aka yi a kan injin din ya zarce wanda aka yi a baya na gwajin injin din rokar mai da iskar gas a kasar Sin, a cewar cibiyar da ta kera injin din a ranar Lahadi a cikin wata sanarwa. (Yahaya Mohammed)