logo

HAUSA

Rahoto: Zarge-zargen Amurka kan “barazanar kutsen yanar gizo na kasar Sin” kage ne

2024-04-15 10:47:20 CMG Hausa

A safiyar yau ne cibiyar martanin gaggawa kan cutar kwamfuta ko computer virus a Turance ta kasar Sin ta fitar da wani rahoto mai taken “Volt Typhoon- tsarin damfarar hukumar leken asiri a kan majalisar dokokin Amurka da masu biyan haraji”. Rahoton ya fallasa babbar badakala inda hukumar leken asirin Amurka suka yi amfani da abin da ba shi da tushe balle makama na abin da suke kira "barazanar kutsen yanar gizo na kasar Sin" a matsayin uzuri na bata wa kasar Sin suna ba tare da wani dalili ba, domin samun kudi daga Amurka.

A ranar 1 ga watan Fabrairun wannan shekara, majalisar wakilan Amurka ta yi wani zaman sauraren bahasi kan abin da suke kira "barazanar kutsen yanar gizo na kasar Sin ". Taron ya mayar da hankali ne kan kungiyar masu kutse ta "Volt Typhoon" wadda Microsoft ta bayyana a watan Mayun 2023. Microsoft ya yi ikirarin cewa kungiyar masu kutsen "tana da goyon bayan gwamnatin kasar Sin" kuma ta yi ikirarin cewa ta yi kutsen yanar gizo kan muhimman ababen more rayuwa a Amurka da kuma yunkurin kara lalata su, wanda ke zama babbar barazana ga tsaron kasar Amurka. A matsayin martani ga wanann zargi, tawagar hadin gwiwar binciken fasaha ta kasar Sin ta gudanar da wani bincike don bin diddigin lamarin inda aka gano cewa, babu wata shaidar da ta tabbatar da zarge-zargen da ake yi, kuma an tsara su ne kawai da kuma kage, da nufin murkushe kima da ci gaban kasar Sin. (Yahaya Mohammed)