logo

HAUSA

An gama bikin baje kolin sabbin makamashi na yankin bakin kogin Yangtse na kasar Sin

2024-04-15 10:16:39 CMG Hausa

A jiya Lahadi ne aka rufe bikin baje kolin sabbin makamashi na yankin bakin kogin Yangtse na kasar Sin na shekarar 2024 a birnin Ningbo na lardin Zhejiang. Babban taken baje kolin ne na bana shi ne “Raya sana’o’i ta hanyoyin kare muhalli, don kafa makoma mai haske”, baje kolin ya samu halartar kamfanonin sabbin makamashi sama da guda 100 daga kasashe daban daban, inda aka nuna kayayyaki na fannonin makamashin hydrogen, da samar da wutar lantarki ta hasken rana, da makamahsin zafin rana, da motoci masu aiki da wutar lantarki da sauransu. Kana, kamfanoni masu sayayya sama da guda 40 daga kasashe da yankuna sama da 20 sun zo baje kolin, domin tattauna kan harkokin kasuwanci, tare da kulla yarjeniyoyin da darajarsu ta zarce RMB Yuan biliyan daya, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 138. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)