Mene ne dalilin da ya sa Japan ke daukar wasu matakan da ka iya haifar da hadari?
2024-04-14 21:07:42 CMG Hausa
A kwanan nan kasar Japan ta rika daukar wasu matakan da ka iya haifar da hadarin gaske, ciki har da kara karfafa yarjejeniyar tsaro tsakanin ta da Amurka a wasu manyan fannoni, da hada kai tare da kasashen Amurka, da Australiya, da Philippines, don gudanar da atisayen soja a tekun kudancin kasar Sin, da kuma neman shiga kungiyar AUKUS, al’amarin da ya sha suka sosai daga bangarori daban-daban.
Daga cikin dukkan wadannan abubuwa, abun da ya fi janyo ce-ce-ku-ce shi ne, karfafa kawancen soja tsakanin Amurka da Japan. A wajen taron kolin shugabannin Amurka da Japan da aka yi a birnin Washington a wannan karo, an samu wani gagarumin ci gaba da ba’a taba ganin irinsa ba a shekaru sama da 60 ga yarjejeniyar tsaro ta kasashen biyu, ciki har da yi wa rundunar sojan Amurka dake Japan garambawul, da kara hadin-kai ta fuskar soja, da nufin kawo sauye-sauye ga ayyukan rundunar tsaron gidan Japan, har ta zama “rundunar masu kai hari”, gami da kara dunkule kasashen Amurka da Japan ta fannin aikin soja.
Manazarta na ganin cewa, wadannan sabbin matakan da Japan ta aiwatar, sun shaida cewa, kasar na kara nisanta kanta daga kundin tsarin mulki na kiyaye zaman lafiya, da bada hadin-kai matuka ga manyan tsare-tsaren Amurka, domin kawo cikas ga ci gaban kasar Sin.
Kaza lika, matakan da Japan ta aiwatar sun ja hankulan bangarori daban-daban, inda jaridar “Asahi Shimbun” ta Japan ta ruwaito cewa, ana kara nuna shakku kan kimar Japan, a matsayin wata kasa dake son shimfida zaman lafiya.
A matsayinta na kasa mafi girma ta fuskar aikin soja a duniya, yunkurin Amurka na shiga cikin harkokin yankin Asiya da tekun Pasifik na tattare da dalilan soja. Kuma inganta kawancen soja tsakanin Amurka da Japan, ka iya kawo sauyi ga halin daidaito na yankin, da janyo damuwa, da rashin gamsuwa daga sauran kasashe, da yin barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin. (Murtala Zhang)