logo

HAUSA

Yaki da ta’addanci : Kwararrun malaman sojojin Rasha sun iso Nijar

2024-04-14 17:00:07 CMG Hausa

Tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023, kasar Nijar ta dauki niyyar kara yawaita hanyoyin kulla huldar dangantaka tare da wasu kasashe a fannoni daban daban, inda a kwanan nan hukumomin kasar suka karbi wata tawagar sojojin Rasha.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.  

Dangantakar tsaro tsakanin Nijar da Rasha ta karfafa tare da zuwa a birnin Yamai a ranar Laraba 10 ga watan Afrilun shekarar 2024, da wata tawagar kwararrun sojoji da suka zo domin horar da rundunar sojojin Nijar bisa tsarin yaki da ta’addanci, haka kuma hukumomin kasar Nijar sun karbi wasu kayayyakin soja iri daban daban daga wannan tawaga ta Rasha.

A cewar, talabijin din kasa RTN a ranar Juma’a 12 ga wata da ya bada labarin cewa, kasar Rasha za ta kafa tsarin kariyar samaniya a kasar Nijar, da ke iyar kula da shawagi a sararin samaniya. Haka kuma, a cewar wannan kafar gwamnatin Nijar, kwararrun sojojin Rasha zasu samar da horo mai inganci ga sojojin Nijar domin aiki da wannan na’ura.

Wannan dangantaka tsakanin Rasha da Nijar ta biyo bayan tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugaban Nijar Abdourahamane Tiani da shugaban Rasha, Vladimir Putin a ‘yan kwanakin da suka gabata, kan batun karfafa wannan dangantaka.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.