logo

HAUSA

Shugaban gwamnatin Jamus ya isa Chongqing domin fara ziyarar kwanaki 3 a Sin

2024-04-14 21:35:17 CMG Hausa

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, ya isa birnin Chongqing a yau Lahadi, domin fara ziyarar aiki ta kwanaki 3 a kasar Sin.

Wannan ne dai karo na biyu da mista Scholz ke ziyartar kasar Sin tun bayan hawansa karagar mulki. Shi ne kuma shugaban wata kasar Turai na farko da ya ziyarci kasar Sin a cikin wannan shekara ta 2024. (Saminu Alhassan)