logo

HAUSA

Firaministan Antigua da Barbuda: Kasa dake nuna mana goyon baya mafi girma ita ce Sin

2024-04-13 16:16:45 CMG Hausa

Firaministan Antigua da Barbuda, Gaston Browne, ya yi hira da dan jaridar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin a kwanan nan.

A cikin zantawar, Browne ya bayyana cewa, Sin ta dade tana ba da tallafi ga ci gaban fannoni daban daban na Antigua da Barbuda. A cikin gomman shekaru da suka gabata, kasar dake nuna musu goyon baya mafi girma ita ce Sin. Dangantakar kasashen biyu na daya daga cikin mafi kyawun misalan alakar dake tsakanin babbar kasa da karamar kasa.

Ya kara da cewa, Sin tana da kirki kwarai, ta ba da babbar gudummawa ga zaman lafiya da wadata na kasa da kasa. Kuma ra’ayin gina al’ummun makomar bai daya na daukacin bil’adam da shugaban Sin Xi Jinping ya gabatar, ya karfafa Sin ta ba gudummawar nan, ra’ayin ya kasance wani babban buri ga daukacin dan Adam.

Bugu da kari, ya ce a cikin shekaru goma da suka gabata, Sin ta ba da tallafi mai yawa ga kasashe masu tasowa, domin tallafa musu wajen kara karfi a kan fannoni daban daban, musamman wajen kawar da talauci. (Safiyah Ma)