logo

HAUSA

Jakadan Sin a Nijar ya gana da ministan harkokin wajen kasar

2024-04-13 19:03:32 CMG Hausa

A ranar 11 ga watan Afrilu bisa agogon Nijar, jakadan Sin a Nijar Jiang Feng ya gana da ministan harkokin waje da hadin gwiwar kasar Bakary Yaou Sangare, a birnin Yamai, inda suka yi mu’amalar sada zumunta kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da hadin gwiwa a aikace.

Jiang Feng ya bayyana cewa, kasar Sin na shirya sabon taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Kuma a shirye take ta dauki wannan a matsayin wata dama ta kara karfafa hadin gwiwa a aikace da kasar Nijar a fannonin mai, wasanni, kiwon lafiya, tattalin arziki da cinikayya, da fasahar sadarwa.

A nasa bangaren, Bakary Yaou Sangare ya bayyana fatansa cewa, taron zai iya cimma yarjejeniyoyi da dama, don kara fadada hadin gwiwa tsakanin kasashen Nijar da Sin, da samun moriyar juna da nasara tare. (Yahaya)