logo

HAUSA

Sin ta kasance kan gaba wajen fitar da hajoji a tsawon shekaru 7 a jere

2024-04-13 15:14:05 CMG Hausa

Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana cewa, kasar Sin ta kasance kan gaba wajen fitar da hajoji a shekarar 2023 na tsawon shekaru bakwai a jere, inda take da kaso 14.2 cikin dari, kusan daidai da kason shekarar 2022.

Ma’aikatar ta bayyana hakan ne a matsayin martani ga sabon “hasashe da kididdigar cinikayya na duniya” na hukumar cinikayya ta duniya wato WTO, wanda ke hasashen samun farfadowa sannu a hankali a yawan cinikayyar hajoji a duniya a shekarar 2024 da ta 2025, biyo bayan dan tsukewa da ya yi a shekarar 2023.

Ma'aikatar ta ce, kasar Sin ta kasance kasa ta biyu a kan gaba wajen shigo da kayayyaki a shekarar 2023 tare da kaso 10.6 bisa dari, daidai da matakin shekarar 2022. (Yahaya)