logo

HAUSA

Shugaban gwamnatin kasar Jamus da ministar waje ta kasar Afirka ta Tsakiya za su ziyarci Sin

2024-04-13 16:26:49 CMG Hausa

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a jiya Juma'a cewa, shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz, zai kawo ziyara kasar Sin tsakanin ranar 14 zuwa ta 16 ga watan Afrilu da muke ciki. Ban da haka, ministar harkokin wajen kasar Afirka ta Tsakiya, Sylvie Baïpo Témon, ita ma za ta kawo ziyarar aiki a kasar ta Sin, duk a tsakanin ranar 14 da ta 16 ga wata. (Bello Wang)