logo

HAUSA

Cinikayyar shige da fice ta Sin ta daga da kaso 5% a rubu’in farko na bana

2024-04-12 19:42:44 CMG Hausa

Cinikayyar shige da fice ta Sin ta bunkasa da kaso 5 bisa dari, a rubu’in farko na shekarar nan ta 2024, idan an kwatanta na makamancin lokacin shekarar bara, kamar dai yadda alkaluman da hukumar kwastam ta kasar ta fitar a Juma’ar nan suka tabbatar.

Daga watan Janairu zuwa Maris, cinikin waje na kayyayakin kasar Sin ya kai yuan tiriliyan 10.17 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 1.43, a cewar hukumar kwastam ta kasar. (Yahaya)