logo

HAUSA

Rikici ya barke a birnin Tripoli

2024-04-12 12:46:00 CMG Hausa

Rahotanni daga kasar Libiya na cewa a daren jiya Alhamis, rikici ya auku a Tripoli fadar mulkin kasar. Kawo yanzu an kwantar da kurar rikicin, kana ba a samu rahoton asarar rayuka ba.

Bayan aukuwar lamarin, ma’aikatar kiwon lafiyar kasar ta fitar da wata sanarwa, wadda ke cewa yanzu haka yanayin kwanciyar hankali ya dawo a birnin, kuma babu asarar rayuka ko jikkatar mutane.

Kafofin yada labarai na kasar sun labarta cewa, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar, ya tabbatar da ikirarin da ma’aikatar kiwon lafiyar kasar ta yi, ya kuma ce an girke sojoji da ‘yan sanda, don tabbatar da tsaron birnin.

Ya zuwa yanzu, babu tabbaci game da asalin wadanda ke da hannu a rikicin, ko dalilin aukuwarsa. (Amina Xu)