logo

HAUSA

An yi taro cikin gaggawa kan cutar kyandar biri a Kinshasa

2024-04-12 14:35:54 CMG Hausa

Jiya Alhamis, hukumar kiwon lafiya ta Kongo kinshasa da cibiyar kandagarkin cututtuka ta Afrika wato Africa CDC sun kira babban taron kasashen yankin Afirka kan cutar kyandar biri cikin gaggawa. Mahalarta taron sun yi kira ga kasashen da abin ya shafa da su dauki matakan da suka dace don tinkarar wannan kalubale cikin hadin kai.

Jami’an hukumar kiwon lafiya daga kasashe 12 ciki har da Kongo Kinshasa sun halarci wannan taro mai tsawon kwanaki 3. Ministan kiwon lafiya na kasar Kongo Kinshasa Roger Kamba ya gabatar da jawabi cewa, cutar ta dade tana addabar kasar matuka, wadda har ta kawo barazana ga kasashe da dama dake wannan yanki. A cewarsa, ya kamata kasashe su yi hadin gwiwa don magance matsalar tare.

Babban daraktan Africa CDC Jean Kaseya ya ce, dole ne kasashen su hada kansu don hana Kongo Kinshasa ta zama asalin yaduwar cutar. (Amina Xu)