logo

HAUSA

Xi ya gana da shugaban kasar Suriname

2024-04-12 20:02:23 CMG Hausa

A yau Juma'a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Suriname Chandrikapersad Santokhi a nan birnin Beijing.

Bayan ganawar, shugabannin kasashen biyu sun rattaba hannu kan takardun hadin gwiwa da dama kan zuba jari a fannin tattalin arziki da cinikayya, da bunkasa sha’anin kiyaye muhalli, da tattalin arzikin dijital, da ilimi da dai sauransu. (Yahaya)