logo

HAUSA

Sin ta kaddamar da dandalin hadakar na’urori masu kwakwalwa masu saurin gaske da nufin bunkasa tattalin arziki na dijital

2024-04-12 10:25:56 CMG Hausa

Kasar Sin ta kaddamar da dandalin hadakar na’urori masu kwakwalwa masu saurin gaske, da nufin bunkasa cin gajiya daga fannin tattalin arziki na dijital. An kaddamar da dandalin ne jiya Alhamis a birnin Tianjin na arewacin kasar Sin.

An ce dandalin zai taimaka wajen rage gibin karfin sarrafa bayanai na na’urori daban daban da ake amfani da su, tare da samar da tallafin gina fannin tattalin arziki na dijital.

Kwararre a fannin na’ura mai kwakwalwa, kuma shaihun malami a cibiyar bunkasa ilimin kimiyya ta kasar Sin, kana jagoran kwararrun dandalin Qian Depei, ya ce za a yi amfani da fasahar kirarriyar basira ko AI a matsayin damar ingiza hadin gwiwar kirkire kirkire a fannonin samar da sassan na’urori masu kwakwalwa, da tsarin lissafin gudanar da ayyukan su, da manhajojin su, da hadakar tsarin ayyukan fannin na’urori masu kwakwalwa.

Masu bayar da hidimar manhajoji da tattara bayanai da manhajojin tsara lissafi sama da 200 ne suka shiga dandalin, inda suka bayar da gudummawar sama da hajoji 3,200, masu nasaba da kirkire kirkiren dijital na zamani, ciki har da masana kimiyyar na’ura mai kwakwalwa, da masu samar da fasahohin kwaikwayon ayyukan masana’antu, da na horaswa a fannin kirkirarriyar basira.

Wata sanarwa daga ma’aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin, ta ce tun a watan Afirilun bara ne aka fara aikin gina dandalin na kasa na hadakar na’urori masu kwakwalwa masu saurin gaske. (Saminu Alhassan)