logo

HAUSA

Jarin kai tsaye da Sin ta zuba a Afirka ya samu bunkasuwa a 2023

2024-04-11 19:55:30 CMG Hausa

A yayin taron manema labaru na yau da kullum na ma’aikatar kasuwancin kasar Sin, kakakin ma’aikatar, He Yadong ya bayyana cewa, jarin da kasar Sin ta zuba a Afirka kai tsaye ya samu bunkasuwa a shekarar 2023.

He Yadong ya gabatar da cewa, a cikin ‘yan shekarun nan, zuba jari da hadin gwiwar Sin a Afirka sun samu bunkasuwa cikin koshin lafiya da daidaito. Matsakaicin jarin kai tsaye na shekara-shekara kan masana’antu ya kasance sama da dala miliyan 400, kuma darajar yawan hadin gwiwa a fannin gine-gine ya kasance sama da dala biliyan 37, wanda ke taimakawa ci gaban masana’antu da tsarin habaka tattalin arziki na Afirka.

Har ila yau, wajen taron manema labarai, ya kuma yi kira ga Amurka da ta gaggauta gyara munanan ayyukanta, ta kuma daina murkushe kamfanonin kasar Sin ba tare da dalili ba, bayan da Amurka ta kara kakaba wa karin kamfanonin kasar Sin takunkumi. Ya ce, kasar Sin za ta dauki dukkan matakan da suka dace don kiyaye hakki da muradun kamfanonin kasar Sin da ke fuskantar takunkumin Amurka. (Yahaya)