logo

HAUSA

Sin na adawa da tunanin yakin cacar baki da siyasar karamar kungiya

2024-04-11 20:35:51 CMG Hausa

Yau Alhamis, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Game da taron kolin Amurka da Japan da ake gudanar, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Mao Ning ta bayyana cewa, kasashen Amurka da Japan ba su yi la’akari da damuwar Sin ba, sun yi wa Sin batanci a kan batun yankin Taiwan da abin da ya shafi ikon mallakar teku, kuma sun tsoma baki cikin harkokin cikin gida na Sin.

Game da hakan, Sin ta nuna adawa, kuma ta yi kakkausar suka ga bangarorin da abin ya shafa. Sannan kuma bangaren Sin na adawa da tunanin yakin cacar baki da siyasar karamar kungiya.

Game da sanarwar da shugaban Amurka Joe Biden ya fitar bayan da ya gana da firaministan Japan Fumio Kishida, Mao Ning ta bayyana cewa, damuwar da Amurka da Japan suke nuna wa manufar makaman nukiliya ta Sin, ba ta da tushe, kuma tana da mugun nufi. Sin tana bin manufar kin yin amfani da makaman nukiliya a matsayin zabi na farko, ta yi wa kasashe da yankunan da ba su da makaman nukiliya alkawarin cewa, ba za ta yi amfani da makaman nukiliya a wuraren ba, ta dade da kiyaye karfin nukiliya a karamin matsayin da kasar take bukata, ba za ta shiga kowace takarar makamai ba. Idan dai wata kasa ba ta yi amfani da makaman nukiliya ga Sin ba, to ba za ta ga barazanar makaman nukiliya daga Sin ba.

Game da Falasdinu a hukumance ta bukaci kwamitin sulhu na MDD da ya sake duba bukatarta ta shekarar 2011 ta zama mamba ta MDD, Mao Ning ta ce, Sin na goyon baya ga Falasdinu wajen zama mamba ta MDD, kuma tana goyon bayan kwamitin sulhu ya gudanar da aikin da wuri.

Ban da wannan, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta fitar da wata takarda a yau, inda ta sanar da daukar matakin da ya dace kan wasu kamfanoni biyu na Amurka dake shiga ayyukan sayar da makamai ga yankin Taiwan na kasar Sin.(Safiyah Ma)