logo

HAUSA

Sin ta bayyana rashin jin dadi kan binciken da EU ta yiwa wasu kamfanonin Sin masu samar da wasu hajoji

2024-04-11 16:53:48 CMG Hausa

Babban jami’in hukumar lura da manufofin cinikayyar sassan waje dake karkashin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin, ya bayyana rashin jin dadin bangaren Sin, game da binciken da EU ta yiwa kamfanoni masu kera injin dake samar da makamashi ta amfani da iska dake juya farfela na kasar Sin, a bangaren samun rangwame, da kuma rahoton da EUn ta gabatar mai cewa wai tattalin arzikin Sin na da babbar matsala.

Jami’in ya yi korafin ne a lokacin da ya gana da jami’in kwamitin EU a Brussels, inda ya bayyana cewa, yayin da EUn ta yi binciken, ta murde gaskiya game da ma’anar rangwame, kana ta gudanar da binciken a kudundune, ba bisa adalci ba, lamarin da ya illata yanayin takara cikin daidaito, bisa hujjar yin takara cikin adalci, tamkar dai manufar nan ta ba da kariya.

Ban da wannan kuma, Sin ta bayyana matukar rashin jin dadi game da rahoton da EU ta gabatar a jiya Laraba, wanda ya ce wai tattalin arzikin Sin na fuskantar matukar sarrafa daga gwamnati, har ma farashin kayayyakin masarufi a kasar na da babbar matsala, kana akwai kalubalen rashin daidaito wajen yin takara cikin adalci.

Sin na ganin cewa, a cikin ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya ta WTO, babu ko daya da ta shafi wannan fanni. Amma EU ta kimanta kasuwannin kasar Sin bisa ka’idar da ta tsara ita kanta kadai, lallai wannan ba abin gaskiya ba ne, kuma hakan zai kawo cikas sosai, da rashin tabbaci ga huldar ciniki tsakanin bangarorin biyu. (Amina Xu)