logo

HAUSA

Mutane biliyan 1.334 ne ke karkashin tsarin inshorar kiwon lafiya a kasar Sin

2024-04-11 20:44:23 CMG Hausa

Adadin mutanen da tsarin inshorar kiwon lafiya na asali na kasar Sin ya shafa ya kai biliyan 1.334 a karshen shekarar 2023, wanda ya kai sama da kashi 95 cikin dari na daukacin al’ummar kasar, kamar yadda rahoton kididdiga ya nuna a yau Alhamis.

Kusan mutane miliyan 371 daga cikin wadannan mutane sun kasance karkashin tsarin inshorar kiwon lafiya ga ma'aikatan birane, kamar yadda rahoton da aka bayar kan raya tsarin inshorar kiwon lafiyar kasar Sin a shekarar 2023 ya nuna. (Yahaya)