logo

HAUSA

Sin, Amurka da EU sun cimma sabuwar matsaya game da hadin gwiwar kare ingancin hajojin cinikayya

2024-04-11 12:35:33 CMG Hausa

Hukumar kwastam ta kasar Sin ta ce Sin, Amurka da kungiyar tarayyar turai ta EU, sun cimma sabuwar matsaya ta hadin gwiwar kara kare ingancin hajojin cinikayyar su.

Yayin taron tattaunawa karo na 8 na sassan uku, game da tsaron ingancin hajojin cinikayya da aka bude a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang na gabashin kasar Sin, sassan sun amince da gina tsarin bai daya, da kyautata sanya ido tare, da mayar da hankali ga kare hakkoki da moriyar masu sayayya, kana da kara azama wajen kare daukacin ingancin hajojin sayayya.

Har ila yau, sun amince da gudanar da aikin hadin kai don cimma gajiyar tsare tsaren hadin gwiwa da ake da su, na kare lafiya da tsaron ingancin hajojin sayayya, da amfani da sabuwar matsayarsu wajen neman kafa mizanin kasa da kasa, da karfafa tasirin ka’idojin da ake amfani da su, da raba bayanai masu nasaba da kare hadurra.

Tsarin hadin gwiwar sassan uku, wanda aka kaddamar shekaru 16 da suka gabata, ya haifar da nasarori masu yawa. Inda a shekarar 2023, darajar cinikayyar hajoji ta kasar Sin da Amurka ta kai kudin Sin tiriliyan 1.8, kwatankwacin sama da dala biliyan 250, kana ta Sin da turai ta kai yuan tiriliyan 1.79. (Saminu Alhassan)