logo

HAUSA

Al’ummar musulmin Nijar ta yi bikin sallar Aid El Fitr

2024-04-10 11:03:23 CMG Hausa

A yayin da wasu kasashen duniya, kamar su Najeriya suke bikin karamar sallah a ranar yau Labara 10 ga watan Afrilun shekarar 2024, su musulmin kasar Nijar a ranar jiya Talata 9 ga wata ne suka yi shagulgulan bikin karamar Sallah ko Aid El Fitr a dukkan fadin kasar.

Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Bikin karamar sallah na ranar jiya, ya biyo bayan kwanaki 29 na gudanar da azumi, bayan kuma ganin watan Sha’awal da ke nuna karshen watan Ramadan, a cikin yankunan kasar Nijar baki daya, haka kuma bayan an gano jinjirin watan sallar a wasu garuruwa da birane.

A babban masallancin Jumma’a na Kaddafi da ke birnin Yamai, al’ummar musulmi yara da manya sanye da sabbin tufafi suka kwarara zuwa wannan masallaci domin gudanar da sallar Idi da ta samu halartar shugaban kasa birgadiye janar Abdrouhamane Tiani, mambobin gwamnatin rikon kwarya, mambobin kwamitin ceton kasa na CNSP, tsoffin shugabannin kasa kamar Mahamane Ousmane da Mahamadou Issoufou.

A cikin hudubarsa, shugaban kungiyar addinin musulunci ta kasa, Check Karanta da ya jagoranci sallar Idi ya tunatarwa musulmi da mahimmancin zaman lafiya da nuna kishin kasa, da kuma kiran ‘yan kasa ga girmama magabata. Haka kuma, babban limamin ya kira ga shugabannin kasa da su yi adalci cikin jagorancinsu.

‘Yan Nijar dai, sun yi bikin karamar sallah a cikin wani lokaci na musamman na takunkumin da aka kakabawa kasar, bayan juyin mulki. Haka mutane sun yi fama da tsadar rayuwa, musamman ma hauhawar farashin kayan abinci da na magunguna da sauransu, amma duk da haka ‘yan Nijar sun kasance tsintsiya madaurinki daya domin kawo goyon bayansu ga sabbin hukumomin soja na kwamitin ceton kasa na CNSP.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.