logo

HAUSA

Yawan kudin da za a zuba kan injuna a fannin masana’antun kasar Sin ya zuwa 2027 zai zarce na 2023 sama da 25%

2024-04-10 10:46:45 CMG Hausa

 

Ma’aikatar raya masana’antu da aikin sadarwa, da wasu hukumomi 7 na kasar Sin, sun gabatar da sabon shirin sabunta injuna a fannin masana’antu a jiya Talata. Shirin ya bayyana cewa, ya zuwa shekarar 2027, yawan kudin da za a zuba kan injuna a fannin masana’antun kasar zai zarce na shekarar 2023 fiye da kashi 25 cikin kashi 100.

Aiwatar da wannan shirin zai baiwa kamfanonin kasar jagoranci bisa doka wajen dakatar da yin amfani da wasu tsoffin injuna, tare da amfani da sabbin injuna na zamani. A sa’i daya kuma, za a mai da hankali kan sabunta manhajoji ko “softwares” a Turance da sauran sabbin kirkire-kirkire. (Amina Xu)