logo

HAUSA

Ma'aikatar harkokin wajen Sin: Sin za ta ci gaba da ingiza karuwar tattalin arzikin duniya

2024-04-09 20:33:15 CMG Hausa

Yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Mao Ning, ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda ta yi tsokaci game da kalaman wani masanin ketare, wanda ya rubuta cewa, wata kila saurin karuwar tattalin arzikin Sin ya ninka na Amurka sau biyu a ‘yan shekaru masu zuwa. Mao Ning ta bayyana cewa, game da makomar tattalin arzikin Sin, abin da bangarori daban daban suka amince da shi shi ne, saurin karuwar tattalin arzikin Sin yana kan gaba a tsakanin kasashen duniya mafiya karfin tattalin arziki. 

Ta ce a matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, tattalin arzikin Sin yana da tushe mai karfi, da juriya mai karfi, da kuma babbar damar samun ci gaba.

Game da kalaman sakatariyar baitil-malin Amurka Janet Yellen, na cewa gwamnatin Amurka za ta ja hankalin Sin ga sauya manufofin masana’antun ta dake kawo barazana ga guraben ayyukan yi na Amurka, Mao Ning ta bayyana cewa, daukar batutuwan tattalin arziki da cinikayya, kamar karfin samar da hajoji a matsayin batutuwan siyasa da tsaro, ya sabawa ka’idojin tattalin arziki, kuma ba shi da amfani ga masana’antun Amurka, da ma ci gaban tattalin arzikin duniya cikin kwanciyar hankali.

Game da dangantakar Sin da Rasha kuwa, Mao Ning ta ce, kiyayewa, da bunkasa dangantakar Sin da Rasha, ba ma kawai zabi ne da ba shi da makawa ga kasashen biyu ba, a matsayinsu na kasashe makwabtan juna, har ma ya yi daidai da muhimman muradun al'ummomin kasashen biyu. Kaza lika bangaren Sin na fatan yin aiki tare da bangaren Rasha, wajen karfafa hadin gwiwar tsare-tsare karkashin dandaloli daban daban na kasashen biyu, da gudanar da ra’ayin bangarori daban daban bisa gaskiya, da inganta mulkin kasa da kasa bisa adalci, da tsayawa tsayin daka kan yin adawa da kare ra’ayin bangaranci, da nuna fin karfi, ta yadda za a inganta duniya ta samu makoma mai haske ta zaman lafiya, da tsaro, da wadata da kuma ci gaba. (Safiyah Ma)