logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya zanta da takwaran aikinsa na Micronesia

2024-04-09 19:18:17 CMG Hausa

A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da takwaran aikinsa na kasar Micronesia mista Wesley W. Simina a birnin Beijing.

Kaza lika a dai yau din, shugaba Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, da shugaban jam’iyyar ‘yan kwadago ta Brazil, kuma shugaban kasar Luiz Inacio Lula da Silva, sun aike da wasikun taya murnar gudanar da taron karawa juna sani karo na 7, na tattauna ka’idojin tushe na jam’iyyar kwaminis ta Sin, da jam’iyyar ‘yan kwadago ta Brazil.   (Saminu Alhassan)