logo

HAUSA

Firaministan Kasar Sin Ya Jagoranci Taron Neman Ra’ayi Kan Aikin Tattalin Arziki

2024-04-09 14:46:30 CMG Hausa

A jiya Litinin ne firaministan kasar Sin Li Qiang ya kira taron karawa juna sani da masana tattalin arziki da ‘yan kasuwa, domin neman ra’ayi kan halin da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki, da aikin da za a yi mataki na gaba.

A yayin taron, mahalarta taron sun cimma matsaya cewa, duk da cewa, yanayin tattalin arzikin waje akwai sarkakkiya, kuma ana fuskantar matsaloli da kalubale, tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da samun bunkasuwa mai kyau, tare da kwarin gwiwar kasuwanni.

Bayan sauraron jawabai na mahalarta taron, Li ya amince cewa, yanayin tattalin arzikin waje na kara tsunduma cikin sarkakkiya, tsanani da rashin tabbas. Duk da haka, ya jaddada cewa, kasar Sin ta aza tubali mai kyau wajen raya tattalin arziki, tana kuma da fa'ida iri iri, da kuma manyan damammaki. Ci gaban da ake sa ran Sin za ta samu ba zai canza ba cikin dogon lokaci.

Ya yi nuni da cewa, domin karfafawa da bunkasa kyakkyawan yanayin tattalin arziki, ya zama wajibi a kara kaimi wajen gaggauta aiwatar da manufofin gwamnati, da kara zaburar da kasuwanni, da karfafa ci gaba mai dorewa, da tunkarar manyan matsaloli cikin tsari. (Yahaya)