logo

HAUSA

Rwanda ta nuna damuwa kan yadda Amurka ke nuna shubuha game da wadanda aka yi wa kisan kare dangi a shekarar 1994

2024-04-09 11:31:13 CMG Hausa

 

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame a jiya Litinin ya bayyana matukar damuwarsa kan yadda kasar Amurka ta kasa daukar kisan kiyashin da aka yi a shekarar 1994 a matsayin kisan kare dangi a kan al’ummar Tutsi.

Sukar Kagame ta zo ne bayan jawabin sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken na tunawa da kisan kiyashin. A cikin jawabinsa da ya wallafa a shafin sada zumunta na X, Blinken ya ce, muna jimamin dubban ‘yan kabilar Tutsi, Hutu, Twas da sauran wadanda suka rasa rayukansu a tsawon kwanaki 100 na tashin hankali da ba a taba ganin irinsa ba. 'Yan Rwanda da dama sun soki Blinken saboda rashin amincewa da cewa, an yi wa 'yan kabilar Tutsi kisan kare dangi.

Cece-kuce kan yadda aka bayyana kisan kare dangin, ya samo asali ne daga zargin da ake yi wa sojojin kishin kasar ta Rwanda wato Rwandan Patriotic Army, kungiya ce ta 'yan tawayen da ta dakatar da kisan kiyashin, ta aiwatar da kisan ramuwar gayya a lokacin, da kuma bayan kisan kare dangin. A baya dai, Kagame ya yi watsi da wadannan zarge-zargen.

A cikin jawabinsa na tunawa da kisan kiyashin a Lahadi, Kagame ya ce, 'yan Rwanda ba su taba fahimtar dalilin da ya sa kasashe ke ci gaba da nuna rashin fahimta game da wadanda aka yi wa kisan kare dangin ba, yana mai kiransa wani nau'i na musantawa, kuma wani laifi ne. Ya kara da cewa, Rwanda za ta kalubalanci hakan a ko da yaushe.

A ranar Lahadi ne kasar Rwanda ta fara zaman makoki na mako guda da kuma kwanaki 100 na tunawa da cika shekaru 30 da kisan kare dangi da aka yi wa 'yan kabilar Tutsi a shekara ta 1994, inda aka kashe sama da mutane miliyan 1, a cewar gwamnatin kasar ta Rwanda. (Yahaya)