logo

HAUSA

PLA Ta Gudanar Da Atisayen Hadin Gwiwa A Kan Teku Da Sararin Sama A Tekun Kudancin Kasar Sin

2024-04-09 10:19:57 CMG Hausa

Rundunar ‘yantar da jama’ar kasar Sin (PLA) a sashen kudancin kasar ta gudanar da atisayen hadin gwiwa na sojan ruwa da na sararin sama a tekun kudancin kasar Sin daga ranar 7 zuwa 8 ga watan Afrilu, a cewar babban kanal Tian Junli, mai magana da yawun rundunar ta PLA a sashen kudancin kasar, a cikin wata sanarwa a yau Talata.

Dakarun rundunar a sashen kudancin kasar sun kasance cikin shirin ko-ta-kwana a kowane lokaci, don tabbatar da ikon mulkin kasar Sin da tsaron kasar da kuma hakki da muradun teku na kasar Sin, a cewar Tian. (Yahaya)