logo

HAUSA

Saira Banu, 'yar kasar Pakistan: "Zan tsaya tsayin dak kan cimma burina na ba da gudummawa ga sha’anin koyar da Sinanci a kasarmu "

2024-04-08 15:30:40 CMG Hausa

A watan Nuwamba na shekarar 2022, 'yar Pakistan Saira Banu ta zo Kwalejin kasa da kasa ta Jami'ar Kudu maso Yamma don yin karatun digiri na biyu a fannin koyar da Sinanci ga daliban kasashen waje. Fiye da shekara guda ke nan, Saira Banu ta samu sabon ci gaba, da sabbin abokai, da kuma sabon abun da take ji.

“Wannan lokaci tsawon shekara guda yana da muhimmanci sosai a gare ni, kuma na samu ci gaba a fannoni daban daban. Alal misali, na fahimci cewa ina da hakuri fiye da da. Domin a kasar Sin, na samu haduwa da mutane daban-daban daga kasashe daban-daban. Yanzu na koyi yadda zan tausayawa wasu, da yadda zan fahimci yadda wasu suke ji. Na kuma koyi yadda zan ci gaba da kasancewa mai fara’a, da nuna yakini a yayin da nake fuskantar wahalhalu.”

Da take magana game da yadda take karatu a kasar Sin a bana, Saira Banu ta yi magana ba tare da karewa ba. Ta ce,

“A lokacin da na fara zuwa kasar Sin a bara, Sinanci na ba shi da kyau sosai, yanzu ina iya karatu da rubutu da kyau cikin harshen Sinanci, da kuma mu'amala da abokai Sinawa cikin sauki, a fannin ilimi kuma na samu sabbin ilimi da yawa.”

A bana, Saira Banu ta kuma samu abokai da yawa a makaranta, kuma ta kara fahimtar al'adun gargajiyar kasar Sin. Ta shiga ayyukan kulake da yawa, kuma ta fi sha'awar fasahar wasan opera ta Peking ta kasar Sin.

“Na sami ‘yar fahimtar wasu al'adun rubutu da zane-zane, da ma al'adun shayi na kasar Sin. Amma ni kaina, abin da ya fi burge ni shi ne wasan Peking Opera. A jiya jami’armu ta shirya wani aiki game da Peking Opera. Lokacin da na halarci gasar ‘Gadar Sinanci’, wato gasar da ake yi game da Sinanci, na zabi shirin rera wakar Huangmei Opera.”

A wannan shekarar ma Saira Banu ta zama mai masaukin baki a makaranta, kuma ta dauki nauyin ayyukan harabar jami'a da dama.

Ta ce, ayyuka masu kayatarwa da ban sha’awa a jami’ar sun kafa dandalin wasan kwaikwayo daban-daban domin dalibai su nuna kansu, ta gano cewa dalibai da dama sun kware sosai, haka nan kuma karfin ta na furuci da Sinanci ya karu matuka ta hanyar wadannan ayyukan.

“A matsayina na daliba daga kasar waje, ina karbar bakunci da Sinanci da ma Turanci, hakan ya ba ni damar kara gogewa mai yawa, da koyon yadda ake bayyana kaina a kan dandalin wasan kwaikwayo.”

 Saira Banu ta bayyana cewa, a matsayinka na mai masaukin baki, kana bukatar fahimtar dukkan shirye-shiryen, da yin mu’amala da hadin kai tare da sauran membobin, wannan kuma ya inganta iyawar hadin gwiwa, tare da kara kwarewar yin jawabi.

A lokacin hutun bazara da ya gabata, domin sanin al'adu na wurare daban-daban na kasar Sin, Saira Banu ta shafe kwanaki takwas tana balaguro daga birnin Chongqing dake kudu maso yammacin kasar Sin zuwa birnin Kashgar na jihar Xinjiang dake arewa maso yammacin kasar, ta hanyoyin zirga-zirgar ababen hawa daban-daban.

“Ina jin dadin tafiya sosai, don haka lokacin da na dawo Pakistan a wannan bazarar, na yanke shawarar ba zan hau jirgin sama ba, sai na zabi in dauki bas mai yin doguwar tafiya. Ta haka zan iya ganin sauran wurare masu kyau a kasar Sin, kuma in ga yadda salon rayuwarsu yake.”

Saira Banu ta ce, ta hau jirgin sama daga birnin Chongqing zuwa birnin Urumqi na jihar Xinjiang, inda ta yi kwana guda a can, ta dandana abincin musamman nasu, ta kuma gwada al'adunsu, har ma ta yi rawa irin tasu tare da su. Daga nan kuma, ta hau jirgin kasa na sa'o'i 12 daga Urumqi zuwa Kashgar. Ta yi wasa na kwana daya a Kashgar, kuma ta dandana duk abin da suke ci da sutura. Ta gano cewa, mutanen Kashgar suna son yin kade-kade da raye-raye tare, maza da mata suna rawa tare, kuma yanayin wurin yana da kyau sosai.

Bayan ta yi karatu a kasar Sin na tsawon shekara guda da wani abu, Saira Banu ta kara fahimtar yanayin ilimi, da yanayin koyo na kasar Sin.

“Kasar Sin tana da albarkatun ilimi da yawa, da suka hada da makarantu masu inganci, malamai da na’urorin koyarwa. Dangane da ra’ayin ilimi, kasar Sin ta mai da hankali kan koyar da cikakkiyar kwarewa ga dalibai a dukkan fannoni. Har ila yau, dalibai Sinawa suna sha’awar koyon ilmi kwarai da gaske, wadanda ke da kwarin gwiwa ga koyon ilmi.”

Bayan shafe shekara guda tana karatu, Saira Banu ta kara azama kan burinta na sana'a, inda ta ce, tana fatan za ta zama malama mai kwarewa ta koyar da Sinanci a nan gaba.

A yayin hirar, Saira Banu ta ba da kai wajen karanta wata waka ta yaba zumuncin da ke tsakanin Pakistan da Sin, inda ta ce baya ga abokantaka, wannan waka ta kuma nuna irin kaunar da take yiwa harshen Sinanci da kuma kokarin da take yi na cimma buri.

“Na san zan dauka tsawon lokaci kafin cimma burina, amma zan dage kuma in yi aiki tukuru a kai.”

Saira Banu ta ce, tana so ta zama wata malama mai koyar da Sinanci, kuma za ta yi amfani da ilimin da ta koya a kasar Sin a ayyukan koyarwa. Baya ga haka, tana kuma fatan taka rawa ga kasarta ta Pakistan, da ma ayyukan koyar da Sinanci ga daliban kasashen waje, wadanda za kuma su kacance babbar nasara da za ta ci a rayuwarta.