logo

HAUSA

Sin na adawa da kudurin Amurka na girke makamai masu linzami a yankin Asiya-Pasifik

2024-04-08 19:43:02 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta ce Sin na adawa da kudurin kasar Amurka na baya bayan nan, na girke tsarin kaddamar da makamai masu linzami masu cin matsakaicin zango a yankin Asiya-Pasifik.

Mao Ning ta bayyana hakan ne a yau Litinin, yayin taron manema labarai na yau da kullum. Ta ce Sin na nacewa bin hanyar ci gaba cikin lumana, tana tsayawa tsayin daka kan manufofin tsaron kasa na kare kai, kuma ba ta da sha’awar yin takara da kowace kasa don nuna karfin soja. 

Jami’ar ta kara da cewa, bangaren Sin ya dade da bayyana adawa da matakin Amurka na tabbatar da samun fifikon aikin soja na bai daya, ta hanyar girke makamai masu linzami masu cin matsakaicin zango a yankin Asiya-Pasifik, wato karfafa ajiye kayayyakin aikin soja a gaban kofar kasar Sin. Bangaren Sin ya kalubalanci bangaren Amurka da cewa, ya kamata ya mutunta tsaron sauran kasashen duniya, ya kuma daina gurgunta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Game da sabuwar mamba za ta shiga tsarin dangantakar abokantakar tsaron Amurka-Birtaniya-Australia, Mao Ning ta ce, bangaren Sin na adawa da matakin wasu kasashe na kafa kananan gungu, da nufin rura wutar fito-na-fito tsakanin sassa daban daban. Musamman ma Japan, wadda kamata ya yi ta yi koyi da darussan tarihi, ta kuma yi taka-tsantsan wajen furta kalamai, da ayyukan a fagen tsaron aikin soja. 

Game da rikicin Ukraine kuwa, Mao Ning ta ce bangaren Sin ya dade da himmatuwa wajen ba da gudummawa ga tsagaita bude wuta, da warware rikicin ta hanyar siyasa. Har ila yau, Sin za ta ci gaba da ingiza tattaunawar zaman lafiya bisa kwazonta, kuma za ta ci gaba da mu’amala da bangarorin da abin ya shafa, da suka hada da Rasha, da Ukraine, don inganta warwaren rikicin ta hanyar siyasa ba tare da bata lokaci ba. (Safiyah Ma)