logo

HAUSA

Philippines tana kan wata hanya mai hadari

2024-04-08 14:23:25 CMG Hausa

Jiya Lahadi, kasashen Amurka da Japan da Australiya da Philippines sun yi hadin kan gabatar da atisayen soja a tekun kudancin kasar Sin. Kafofin yada labarai na Philippines sun ruwaito cewa, kasashen hudu sun nuna karfin sojinsu a fili, don tinkarar kasar Sin. Philippines tana son dogara da karfin kasashen waje kan batun tekun kudancin kasar Sin da ma jawo hankalin kasa da kasa, duba da taron kolin kasashen Amurka da Japan da Philippines da za a gudanar a Washington. A tsakar wannan rana, rundunar sojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin reshen kudancin Sin ya gudanar da sintiri na teku da sama nan da nan, Sin ba za ta bar kowa ya tada zaune tsaye a tekun kudancin kasar ba.

Tun shekarar bara, Philippines ta yi ta kutsa kai cikin sararin teku dake kusa da tsibirin Huangyan da sashen tudun ruwa na Ren’ai Jiao don tada hankali. Kwanan baya, ta kutsa cikin sashen tudun ruwa na Wire the reef, har ta gudanar da haramtaccen aiki a sararin tekun dake dab da sashen tudun ruwa na Houteng wato “Iroquois Reef”. Mene ne dalilin Philippines game da wadannan matakan da ta dauka, wasu manazarta na ganin cewa, tana son tsanantar da halin da ake ciki a wannan yanki ne har ya jawo hankalin kasa da kasa.

Philippines ta kan bayyana yadda take kishin zaman lafiya a yankin, amma ainihin matakin da ta dauka na tada zaune tsaye ne. Hakikanin dalilin da ya haddasa hakan shi ne wasu kasashe suna rura wuta da ma goyon bayan kasar. An ce, Philippines na matukar dogaro da kasashe masu karfi a bangaren soji da tsaro, kuma su wadannan kasashe suna sarrafa Philippines ta hanyar ba da tallafi da yin atisayen soja da sintiri cikin hadin kai da sauransu. Manufar Philippines game da batun tekun kudancin Sin yanzu, tana zama abin da Amurka ke amfani da shi wajen dakile kasar Sin. Kuma matukar dogaran da Philiphines take yi wa sauran kasashe na jefa ta cikin wani yanayi mai hadari. (Amina Xu)