logo

HAUSA

Minista: Tasirin EV na kasar Sin a kasuwa kwata-kwata ba ya dogara da tallafi

2024-04-08 14:42:21 CMG Hausa

Wang Wentao, ministan kasuwanci na kasar Sin ya bayyana a jiya Lahadi cewa, saurin bunkasuwar kamfanonin kera motocin lantarki (EV) na kasar Sin, sakamakon kirkire-kirkiren fasahohin zamani ne, da kyakkyawan tsarin samar da kayayyaki, da ingantacciyar takara a kasuwa, ba tallafi ba.

Zargin da Amurka da Turai ke yi na samar da motocin fiye da kima ba shi da tushe, a cewarsa.

Wang ya kara da cewa, bunkasuwar masana'antar EV ta kasar Sin ta ba da muhimmiyar gudummawa wajen tinkarar sauyin yanayi a duniya, da samar da sauye-sauye don kiyaye muhalli da rage hayakin Carbon mai dumama yanayi, kuma gwamnatin kasar Sin za ta ba da hadin kai ga kamfanoni wajen kiyaye hakkinsu da moriyarsu.

A yayin da ake fuskantar kalubale da rashin tabbas daga waje, Wang ya ce kamata ya yi kamfanoni su kara karfinsu na cikin gida, da kiyaye kirkire-kirkire, da karfafa iya sarrafa hadarurruka, da dora muhimmanci ga kiyaye muhalli.

Ya kara da cewa, ya kamata kamfanonin kasar Sin su shiga a dama da su wajen ba da gudummawa ga sauye-sauye masu nasaba da kiyaya muhalli a duniya. (Yahaya)