logo

HAUSA

Xi Jinping ya gana da shugaban asusun Merieux na kasar Faransa

2024-04-08 14:42:59 CMG Hausa

Yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da Alain Merieux, shugaban asusun Merieux na kasar Faransa, da uwargidansa a babban dakin taron jama’a da ke birnin Beijing.

Xi Jinping ya jinjinawa taimakon da Alain Merieux da uwargidansa da ma asusun Merieux suka dade suka baiwa bunkasuwar huldar kasashen biyu da ma sha’anin kiwon lafiya a nan kasar Sin.

Xi Jinping ya kuma nanata cewa, Sin na darajanta zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu, yana mai fatan zurfafa mu’ammala tsakanin shugabannin kasashen biyu, ta yadda za a ingiza huldar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. A cewarsa, kasashen biyu sun cimma nasarori masu armashi wajen hadin gwiwarsu a bangaren kiwon lafiya, yana maraba da asusun Merieux da ya ci gaba da zurfafa hadin gwiwa tare da kasar Sin.

A nasa bangaren, Alain Merieux ya ce, “zumuncina da Sin ya fara ne daga shekaru 46 da suka gabata, a cikin wadannan shekaru, ina bibiya da jinjinawa ci gaban da Sin take samu, asusun zai ci gaba da karfafa dankon zumunci tsakanin kasashen biyu da ma ciyar da hadin gwiwarsu a fannin kiwon lafiya gaba.”(Amina Xu)