logo

HAUSA

Xi ya gana da shugaban majalisar dokokin Vietnam

2024-04-08 15:26:29 CMG Hausa

A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban majalisar dokokin Vietnam Vuong Dinh Hue, a nan birnin Beijing.

Xi ya ce, abu mafi muhimmanci a dangantakar dake tsakanin Sin da Vietnam shi ne, bangarorin biyu suna da makamancin ra’ayi da makoma guda, kuma sun kasance ‘yan uwa masu gwagwarmaya tare, wanda hakan ya bayyana dadadden zumunci tsakanin kasashen biyu da ma jam’iyyunsu.

Ya bukaci bangarorin biyu da su yi hadin gwiwa wajen inganta karin nasarori wajen gina al’ummar Sin da Vietnam mai kyakkyawar makomar bai daya, da kyautata zamanatarwarsu, da kara samar da moriya ga jama’ar kasashen biyu, da ba da gudummawa sosai ga sha’anin gurguzu na duniya. (Yahaya)