logo

HAUSA

Jakadan kasar Nijar da ke birnin Alger ya amsa kiran ma’aikatar harkokin wajen kasar Aljeriya

2024-04-08 12:00:54 CMG Hausa

 

A ranar jiya 6 ga watan Afrilun shekarar 2024, aka fitar da wata wasikar da ke bayyana, amsa kiran jakadan jamhuriyyar Nijar da ke birnin Alger na kasar Aljeriya, Aminou Malam Manzo, a ma’aikatar harkokin wajen kasar Aljeriya.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu ya duba wannan takarda, ga kuma rahoton da ya aiko mana.

A ranar Alhamis 4 ga watan Afrilun shekarar 2024 din ta gabata, jakadan Nijar Aminou Malam Manzo ya gana da babbar darektar reshen Afrika, Madam Selma Malika Haddadi.

Tattaunawar ta mai da hankali musamman ma kan dangantaka tsakanin kasashen biyu kan batun kwaso ‘yan Nijar da ke Aljeriya ba bisa doka ba. Hukumomin Nijar sun soki lamarin wannan dangantaka, da suke ganin bangaren Aljeriya ba ya girmamawa.

Madam Selma Malika Haddadi, ta tunatarwa jakadan Nijar da kasancewar wani tsarin dangantaka kebabbe kan wannan matsala ta kwaso mutane. Tare da nuna masa cewa wannan tsarin ya kamata ya kasance wani dandalin sulhu da tattauna abubuwan da ke nasaba da wannan matsala.

Haka zalika, ta sake jaddadawa jakadan Nijar niyyar kasar Aljeriya na girmama sharudan zaman makwabtaka, da kuma niyyar kasarta na ci gaba daidaita da kula da wannan matsala da ta shafi kwararar bakin haure tare da kasar Nijar, da ma sauran wasu batutuwa, cikin girmama juna da dokokin kasa da kasa game da huldar dangantaka, cikin yarda da juna da kuma zumunci.

A makon da ya gabata ne, ministan harkokin wajen Nijar, Bakary Yaou Sangare ya kira jakadan kasar Aljeriya da ke Nijar domin yin allawadai da cin zarafin da ake ma ‘yan Nijar da suka je Aljeriya ba bisa doka, da kuma yadda hukumomin Aljeriya su kwaso su zuwa Nijar ba tare da girmama dokokin kasa da kasa da na makwabtaka ba.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.