logo

HAUSA

Kamfanin kasar Sin ya samu takardar shaidar samar da jirgin saman fasinja mara matuki na farko a kasar Sin

2024-04-08 11:09:06 CMG Hausa

Kamfanin kera jirage marasa matuka na kasar Sin EHang a ranar Lahadi ya samu takardar shaidar iznin kera jirgin sama mara matuki mai jigilar fasinja EH216-S daga hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Sin (CAAC) a Guangzhou, babban birnin lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin.

Ita ce takardar shaidar kera jirgin sama na fasinja mai sarrafa kansa ta farko da aka bayar a kasar Sin, kuma na farko a masana’antar tashi da saukar jiragen sama ta lantarki (eVTOL) ta duniya.

Hu Huazhi, wanda ya kafa kuma shugaban kamfanin EHang, ya ce, samun takardar shaidar jirgin wani muhimmin ci gaba ne ga samfurin jirgin na EH216-S don shiga matakin samarwa cikin adadin mai yawa, da kuma matakin da ya dace ga EHang don ciyar da harkokin kasuwancin jirgin gaba.

Bisa kididdigar da hukumar CAAC ta fitar, girman tattalin arzikin kasar Sin a fannin jiragen saman fasinja masu tashin gajeran tazara ya zarce yuan biliyan 500 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 70.47 a shekarar 2023, kuma ana sa ran zai kai yuan triliyan 2 nan da shekarar 2030.

EH216-S yana da matsakaicin saurin tafiya na kilomita 130 a kowace awa, matsakaicin iyakar tafiya kilomita 30, da matsakaicin lokacin tashi na mintuna 25. EHang ya samar da jimillar jiragen EH216-S 52 a cikin 2023. (Yahaya)