logo

HAUSA

Firaministan Sin ya gana da sakatariyar bailtil-malin Amurka

2024-04-07 20:20:21 CMG Hausa

A yau Lahadi ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya gana da sakatariyar bailtil-malin Amurka Janet Yellen a birnin Beijing.

Yayin ganawar da suka yi, firaminista Li ya yi fatan Amurka za ta martaba sanannun ka’idojin tafiyar da tattalin arzikin kasuwanni, ciki har da gudanar da takara mai tsafta, da hadin gwiwa a bude, da kauracewa juya batutuwan tattalin arziki da cinikayya zuwa na siyasa ko tsaro, kana ta rika hangen nesa game da matsayin karfin samar da hajoji, tare da kallon su ta fuskar bukatun kasuwa, da mahangar cudanyar kasa da kasa.

Ya ce bunkasar sashen sabbin makamashi na Sin, zai ba da muhimmiyar gudummawa ga fannonin kare gurbatar yanayi, da takaita fitar da iskar carbon mai dumama yanayi.

A nata bangare kuwa, Yellen cewa ta yi bisa hadin gwiwar Sin da Amurka, alakar sassan biyu tana kara daidaita. Kuma a matsayin su na manyan kasashe biyu masu karfin tattalin arziki, kamata ya yi Amurka da Sin su iya sauke nauyin dake wuyan su ta fuskar daidaita alakar tattalin arzikin su.

Jami’ar ta kara da cewa, Amurka na jinjinawa ci gaban da aka samu a fannin tattaunawa, da hadin gwiwar raya tattalin arziki tsakanin kasashen biyu, kana Amurka ba ta da burin raba-gari da Sin. (Saminu Alhassan)