logo

HAUSA

Matasan Najeriya da dama su ke zuwa ci rani a yankin Agadez

2024-04-07 14:49:30 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, daruruwan matasan arewacin Najeriya suke shiga yankin Agadez da sunan ci rani, wata damar da za ta ba su aikin yi, ko tafiyar da sana’o’i da aikace aikace domin samun kudin shiga.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya duba wannan batu, ga kuma rahoton da ya hada mana.

Su tsakanin dari biyu zuwa dari uku ne, na matasan Najeriya da ke ketara iyakokin Nijar a kowane mako, domin neman aiki da wasu ayyukan nema kudin shiga. Alhaji Kallid, wakilin kungiyar mazauna ‘yan Najeriya da ke zaune a Agadez.

“Ga cikin ‘yan shekaru biyu zuwa yanzu ana samun bullowar matasa sosai a kan baya. Saboda yanzu a kalla mutane da suke shigowa ba ‘yan kadan ba ne, wadanda suke baro Najeriya suke shigowa nan. Wasu da niyyar su wuce su yi gaba, wasu kuma da niyyar su zo nan su tsaya, su yi harkar kasuwanci, da yanayi da ke fito shi daga gida. Maza da mata, kiyasin da za mu iya yi a kalla a rana, an samu baki, sai an samu sama da mutum dari.”

A cewar matasa da dama da aka hiranta tare da su, hauhawar farashi da matsalar tattalin arziki, da kasar tasu ke fuskanta shi ne dalilin wannan kaura nasu zuwa kasashe da ke makwabtaka da kasarsu, kamar Nijar.

“Gaskiya, ni dalilina, ka ga na farko matsalar tsadar rayuwa, ga ka da ‘yan uwa, kana so ka yi aure, kana ma da shi, sana’arka ba za ta iya rike ka ba. Amma idan ka baro can, ka zo nan, ko yaya dai za ka dinga dan turawa kuma kana ajewa.”

“E gaskiya akwai halin matsewa da matasa suka shiga a Najeriya, wanda darajar Naira ta kare, za ka zo, za ka samu abu ka saya yau, in ka saya kafin minti biyar, za ka zo ka ga abu ya daga ya wuce inda kake tunani.”

A yau, matasa majiya karfi ne ‘yan Najeriya da suka samu zama a Agadez suke gudanar da ayyukan samar da kudin shiga.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.