logo

HAUSA

Sojojin Sin Da Amurka Sun Gana A Hawaii Don Tattauna Batun Tsaron Teku Da Na Sararin Sama

2024-04-06 16:04:17 CMG Hausa

Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta bayyana a yau Asabar cewa, sojojin kasashen Sin da Amurka sun yi taro a Hawaii daga ranar 3 zuwa 4 ga watan Afrilu, inda suka tattauna yanayin tsaron teku da sararin sama tsakanin kasashen biyu.

Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta ce, tawagar aiki ta kasashen Sin da Amurka kan tsarin tattaunawar tsaro da aikin soja kan teku wato MMCA a takaice ta gudanar da taron ne da nufin aiwatar da muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma da kara azama kan ci gaban dangantaka mai dorewa tsakanin sojojin kasashen biyu ba tare da wata matsala ba.

Taron da aka yi a Hawaii, shi ne irinsa na farko da sojojin kasashen 2 suka hadu a waje guda a cikin shekaru da dama da suka wuce. Sojojin kasashen 2 sun gudanar da taron a watan Disamban shekarar 2021 ne ta kafar bidiyo.

A yayin taron na Hawaii, bangarorin biyu sun duba yadda ake aiwatar da ka’idojin matakai masu dacewa da ake dauka sakamakon haduwar sojojin kasashen 2 a sararin sama kan teku, tun bayan taron MMCA na shekarar 2021 da kuma tattauna matakan da za a dauka don inganta batun tsaro kan teku tsakanin kasashen biyu.

Bangaren kasar Sin ya sanar da Amurka a yayin taron cewa, yana matukar adawa da duk wani mataki da ke kawo cikas ga 'yancin kai da tsaron kasar Sin, da sunan 'yancin zirga-zirgar jiragen ruwa da jiragen sama, kuma za ta ci gaba da mayar da martani ga dukkan matakai masu hadari da tsokana kamar yadda doka ta tanada. (Yahaya)