logo

HAUSA

An gudanar da bikin kaddamar da majalissa ta 6 ta kungiyar ECOWAS a tarayyar Najeriya

2024-04-06 16:56:35 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci kasashe mambobin kungiyar ECOWAS da su hada kansu domin yakar duk wani abun da zai iya kawo rarrabuwar kawunan su.

Ya bukaci hakan ne lokacin da yake jagorantar bikin kaddamar da majalissa ta 6 ta kungiyar ECOWAS a birnin Abuja, ya ce samun haduwar kawunan abun ne da ya wajaba domin kara karfin kungiyar musamman a wannan mawuyacin hali da ake ciki.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kara jaddada cewa, kasashe mambobin kungiyar ta ECOWAS ba za su taba ci gaba da zuba ido ba a daidai lokacin da al’umomin kasashen ke fuskantar barazanar rarrabewa.

Shugaban na tarayyar Najeriya wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ta ECOWAS ya ci gaba da bayanin cewa, dole ne ’ya’yan kungiyar su kara dunkulewa waje guda, ta yadda babu abin da zai iya yin tasiri wajen rabuwar kawunan su, inda ya ce babu wata nahiya da za ta iya daidaita al’amura a kasashen mu face mu da kan mu.

“Ba za mu taba cin nasara ba ba tare da bayar da gudummawa ta hakika da kuma jajircewar hukumomin majalissun kasashen kungiyar ECOWAS ba, bugu da kari domin tabbatar da cimma muradun kungiyar na shekara ta 2050, muna bukatar shigowar jama’a sosai cikin tsare-tsaren zartar da al’amura na kungiyar, kuma za a iya cimma hakan ne kawai ta hannun zababbun ‘yan majalissa wanda kuma suke a matsayin ‘yan majalissar kungiyar ta ECOWAS, wanda muke tare da su a nan domin hidimtawa al’ummar yammacin Afrika.”

Jim kadan da kammala bikin kaddamar da ‘yan majalissar, an zabi mataimakin shugaban majalissar dattawan Najeriya Sanata Barau Jibril a matsayin mukaddashin kakakin majalissar kungiyar ta ECOWAS.(Garba Abdullahi Bagwai)