logo

HAUSA

Hukumar lura da aikin hajji a tarayyar Najeriya ta kulla yarjejeniya da kamfanonin jiragen sama game da aikin hajjin 2024

2024-04-05 16:53:44 CMG Hausa

Hukumar lura da aikin hajji a tarayyar Najeriya ta kulla yarjejeniya da manyan kamfanonin jiragen sama wajen jigilar mahajjatan kasar a aikin hajjin shekara ta 2024.

A lokacin da yake sanya hannun ranar Alhamis 4 yayin wani kwarya-kwaryar taro a harabar hukumar dake birnin Abuja, babban birnin Najeriya, shugaban hukumar Malam Jalal Ahmad Arabi ya bukaci kamfanonin jiragen da su tabbatar da cika alkawari wajen jigilar alhazan zuwa kasar Saudiyya da kuma dawo da su gida Najeriya, bayan an kammala aikin hajjin a kan lokacin da aka kayyade.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Shugaban hukumar aikin hajjin ta tarayyar Najeriya ya bayyana kamfanonin jiragen a matsayin daya daga cikin ginshikai mafiya mahimmanci wajen tabbatar da nasarar aikin hajji, a don haka ya bukace su da su yi kokari wajen fita kunyar hukumar da kuma alhazan Najeriya.

Ya ce a lokutan baya, kusan kaso 50 na kalubalen da hukumar ta yi ta cin karo da su, suna da nasaba da matsalolin wasu kamfanonin jiragen, lamarin da ya tabbatar da cewa, a wannan lokaci hukumar ba ta tunanin cin karon da irin wadancan matsaloli sabo da managartan tsare-tsaren da ta dauki lokaci tana yi, domin ganin al’amura sun tafi dai-dai a aikin hajjin na 2024.

Malam Jalal Ahmed Arabi ya shaidawa shugabannin kamfanonin jiragen da aka zaba domin jigilar alhazan na Najeriya cewa, akwai kamfanonin da yawa da suka nuna bukata, amma ba su sami dama ba.

“Hakika Hukumar NAHCON za ta shiga yarjejeniya da ku, amma babban abun da ake tsammanin samu daga wannan yarjejeniya shi ne amana, mun san cewa akwai irinku da yawa da suka nuna sha’awar a ba su aikin hidimar jigilar alhazan, amma ku ne kuka sami nasara daga aikin tantancewar da aka yi bisa la’akari da cancanta, muna fatan za ku nunawa ‘yan Najeriya da duniya baki daya aiki na bajinta kuma mai kyau.”(Garba Abdullahi Bagwai)