logo

HAUSA

Isra’ila ta kirawo karin sojoji don karfafa rundunar tsaron sararin sama kasar a tsaka da tashin hankali da Iran

2024-04-04 16:41:09 CMG Hausa

Rundunar sojin Isra’ila ta sanar a jiya Laraba cewa, tana kara karfafa tsarin tsaronta na sararin sama tare da sojojin share-fage, a yayin da ake ci gaba da samun takun saka tsakanin Isra’ila da Iran.

A cikin wata sanarwar da ta fitar, rundunar sojin ta ce, an yanke shawarar kara yawan ma’aikata da kuma kiran sojojin da ke ajiye don karfafa aikin rundunar tsaron sararin sama ta Isra’ila wato IDF a takaice. Ta kara da cewa, matakin ya biyo bayan tantance halin da ake ciki ne.

A dayan bangaren kuma, a ranar 3 ga wata ne kamfanin dillancin labaran kasar Iran ya ce, a wata tattaunawa da ya yi da shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ta wayar tarho, shugaban Iran Ibrahim Raisi ya yi Allah-wadai da yadda kasashen yammacin duniya ke ci gaba da bayar da tallafin kudi da makamai ga Isra'ila, tare da sanin cewa ba ta bin ka'idojin jin kai da na duniya.

Bashar al-Assad ya ce, Isra'ila na ci gaba da aikata "zalunci da laifuka" a Falasdinu, Siriya da Lebanon, wanda ya saba wa dokokin kasa da kasa. Ya jaddada cewa, kasashen Siriya da Iran sun yi imanin cewa, Isra'ila na kawo cikas ga tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da ma duniya, don haka ya zama wajibi a karfafa hadin gwiwa a  yankin da kasa da kasa a wannan fanni. (Yahaya)