logo

HAUSA

Masanin dokokin kasa da kasa na Birtaniya: Sin tana da ikon mallakar tsibiran yankin kudancin tekun Sin

2024-04-04 16:23:08 CMG Hausa

A kwanakin baya, masanin dokokin kasa da kasa na kasar Birtaniya Anthony Carty, wanda ya rubuta littafin “Tarihi da ikon mallakar yankin kudancin tekun kasar Sin”, ya bayyana cewa, tsibiran yankin kudancin tekun kasar Sin, muhimmin yanki ne kuma mallakin kasar Sin tun can baya, kasar Sin tana da ikon mallakarsu bisa tarihi da dokoki.

A gun taron tattaunawa da aka gudanar a birnin Beijing a kwanakin baya, Carty ya yi bayani game da yadda ya rubuta littafin “Tarihi da ikon mallakar yankin kudancin tekun kasar Sin”. A cikin shekaru fiye da 10, Carty ya karanta fayil na kasashen Faransa da Ingila da Amurka game da ikon mallakar tsibiran yankin kudancin tekun Sin tun daga karshen karni na 19, da yin bincike kan wurin da kansa, ya takaita tarihi da yanayin ikon mallakar tsibiran, da sanin batun ikon mallakarsu, shaidun sun tabbatar da cewa, Sin tana da ikon mallakar tsibiran yankin kudancin tekun Sin, aikinsa ya samar da shaidu masu muhimmanci kan nazarin ikon mallakar tsibiran bisa tarihi da dokoki. (Zainab Zhang)