logo

HAUSA

Xi Ya Taya Sabuwar Shugabar Malta Murnar Kama Aiki

2024-04-04 20:34:35 CMG Hausa

A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya Myriam Spiteri Debono murnar zama sabuwar shugabar kasar Malta.

Xi ya ce, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Malta shekaru 52 da suka gabata, bangarorin biyu suna mutunta juna a ko da yaushe, kuma suna daidaita mu’amala a tsakaninsu, da nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwa masu muhimmanci da suka shafi moriyar juna, da kuma gudanar da hadin gwiwa mai inganci a fannonin tattalin arziki, kasuwanci da zuba jari, al’adu da ilimi, da kuma kiwon lafiya.

Xi ya kara da cewa, yana matukar mutunta bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Malta, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da sabuwar shugabar kasar, don ci gaba da sada dadadden zumunci, da karfafa hadin gwiwa a aikace a tsakanin kasashen biyu, ta yadda za a sa kaimi ga ci gaban dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da samar da karin moriya ga jama’ar kasashen biyu. (Yahaya)