logo

HAUSA

Fa’idar Tattaunawar Baya Bayan Nan Ta Shugabannin Sin Da Amurka

2024-04-04 19:29:04 CMG Hausa

Masharhanta da dama na ci gaba da tofa albarkacin bakin su, game da tattaunawar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi ta wayar tarho da takwaransa na Amurka Joe Biden da yammacin ranar Talata, zantawar da ta shiga muhimmin tarihi a kokarin da kasashen biyu ke yi na aiwatar da matakan yaukaka dangantaka da fahimtar juna. Kafin tattaunawar ta baya bayan nan, shugaba Xi da Biden sun gana keke-da-keke a tsibirin Bali na Indonesia a shekarar 2022, sun kuma gana a birnin San Francisco na Amurka a watan Nuwamban bara, kana sun zanta sau 5 ta wayar tarho.

Wannan dai tattaunawa ita ce ta farko a tsakanin shugabannin biyu, tun bayan da suka yi ganawar ido da ido a watan Nuwamban bara a birnin San Francisco, kuma ko shakka babu ana sa ran zantawar ta wannan karo za ta taimaka, wajen ingiza cimma burin da duniya ke da shi game da cimma daidaiton dangantaka tsakanin kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya.

Daga tattaunawar shugaba Xi da mista Biden, muna iya fahimtar burin sassan biyu na fatan cimma wasu muhimman kudurori a bana, tare da burin kaucewa sake shiga wata sabuwar turka-turka tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Xi dai ya bayyana manyan kudurorin kasar Sin don gane da dangantakarta da Amurka a bana, yana mai fatan sassan biyu za su martaba matakan wanzar da zaman lafiya, da fifita daidaito, da goyon bayan matakan amincewa juna.

Ko shakka babu idan har kasashen biyu sun amince, tare da aiwatar da alkawuran da suka daukawa juna a ganawar San Francisco, da kuma tattaunawar baya bayan nan, hakan zai ingiza cimma nasarar alakar dake tsakanin Sin da Amurka.

Masu fashin baki na ganin idan har kasashen biyu za su kai ga nasarar kyautata alaka, to wajibi ne su sauke nauyin dake wuyan su, ta hanyar martaba juna, su yi cudanya cikin lumana, kana su rungumi hadin gwiwar cimma moriyar juna, kana su ci gaba da yaukaka alaka bisa daidaito.

Muna iya cewa fa’idar ganawar shugabannin biyu ta kara fito da burin kasar Sin na jaddadawa bangaren Amurka muhimmancin inganta dangantakarsu, da fatan Amurka za ta dakatar da yunkurin danne kamfanonin Sin, kana ta nuna sanin ya kamata don gane da batun zirin Taiwan da tekun kudancin Sin.

A daya bangaren, shugaba Biden ya sha alwashin cika alkawuran da Amurka ta dauka a baya, inda ya jaddada muhimmancin dangantakar Amurka da Sin, yana mai nanata cewa Amurka ba ta neman tada sabon yakin cacar baka, kuma ba ta da muradin sauya tsarin kasar Sin, haka kuma kawancen da take yi da sauran sassa ba ya nufin yi wa Sin taron dangi ko mayar da ita saniyar ware.

Muna iya cewa, idan har kalaman shugaba Biden suka dace da matakan zahiri da Amurka za ta dauka a nan gaba, ko shakka babu sassan biyu za su kai ga cimma nasarar bunkasa kan su, da kuma haifar da babbar fa’ida ga bunkasar tattalin arzikin duniya baki daya.(Saminu Alhassan)