logo

HAUSA

Kasar Sin na Allah wadai da harin da aka kai wa ma’aikatan agaji na kasa da kasa a Gaza

2024-04-03 11:24:02 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin ya bayyana a jiya Talata cewa, kasarsa na adawa da duk wani danyen aiki na illata fararen-hula da kayyayakin more rayuwarsu, wanda kuma ya sabawa dokokin kasa da kasa. Haka kuma, tana tir da harin da aka kai wa ma’aikatan agaji na kasa da kasa a zirin Gaza, tare da jajen rayukan da aka rasa.

Jami’in ya ce, Sin ta bukaci bangarori masu ruwa da tsaki, musamman Isra’ila, da su aiwatar da kuduri mai lamba 2728 na kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya a zahirance, da sauke nauyin da kundin tsarin mulkin MDD ya danka musu, da tsagaita bude wuta ba tare da bata lokaci ba, a wani kokari na kiyaye fararen-hula da ba su ji ba su gani ba, da tabbatar da tsaron al’umma gami da kayyayakin amfaninsu bisa Yarjejeniyar Geneva, ciki har da asibiti, don kaucewa ta’azzarar bala’in jin-kai a zirin na Gaza.

Game da harin ta’addancin da aka kai kan tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa na Dasu da kamfanin kasar Sin ke gniawa a kasar Pakistan a ranar 26 ga watan Maris, Wang ya ce, kasar Sin na tuntubar Pakistan sosai game da wannan batu, don ganin an hukunta ‘yan ta’addan da suka kai harin.

A kwanan nan ne wato ranar 1 ga watan Afrilu, firaministan kasar Pakistan, Muhammad Shahbaz Sharif ya yi tattaki zuwa tashar Dasu don mika gaisuwa da fatan alheri ga ma’aikatan kasar Sin dake wurin, inda ya yi alkawarin cewa, kasarsa za ta yi iya bakin kokarinta wajen kare tsaron Sinawa gami da ayyukan da suke yi, da yanke hukunci mai tsanani kan wadanda suka kai harin. (Murtala Zhang)