logo

HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin ya yi bayani game da tattaunawar shugaba Xi Jinping da Joe Biden

2024-04-03 20:38:30 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya yi karin haske a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau, game da tattaunawa ta wayar tarho, tsakanin shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Joe Biden, kan batutuwan sashen tudun ruwa na Ren’aijiao, da yankin Hong Kong, da jihar Xinjiang, da ta Xizang da sauransu.

Game da batun sashen tudun ruwa na Ren’aijiao, Wang Wenbin ya bayyana cewa, a yayin tattaunawar, Sin ta jaddada cewa, tana da ikon mallakar tsibiran Nansha, da yankin teku dake dab da su, wadanda suka hada da tsibirai da sassan tudun ruwa, da yankunan rairayi, ciki har da sashen tudun ruwa na Ren’aijiao.

Wannan batu dai ya biyo bayan yadda bangaren kasar Philippines ya yi ta sabawa alkawarin da ya dauka, ta hanyar yunkurin kafa sashensa na dindindin a kan tsibirai, da sassan tudun ruwa na kasar Sin da babu mutune a kansu, da nufin sace ikon mallakar sashen tudun ruwan Ren’aijiao. Bangaren Sin na ganin Amurka ba ta da nasaba da wannan batu na yankin kudancin tekun kasar Sin, don haka bai kamata ta tsoma baki cikin batun Sin da Philippines ba.

Game da batun jihar Xinjiang da ta Xizang, Wang Wenbin ya jaddada cewa, batun Xinjiang da Xizang, batu ne na cikin gidan kasar Sin. Kaza lika kasar Sin na dora muhimmanci sosai kan kare hakkin dan Adam. Ya ce, jama’ar kasar ne ke da ikon bayyana ra’ayinsu kan kare hakkin dan Adam na kasarsu.

A daya bangaren, kasar Sin tana fatan yin mu’amala tare da Amurka, kan batun kare hakkin dan Adam bisa tushen girmama juna, sai dai Sin din ba za ta amince da duk wani nau’in aiki na tsoma baki cikin harkokin cikin gidanta bisa hujjar kare hakkin dan Adam ba. (Zainab Zhang)