logo

HAUSA

Xi Jinping da Joe Biden sun tattauna ta wayar tarho

2024-04-03 10:28:49 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na Amurka Joe Biden a jiya Talata ta wayar tarho, bisa bukatar shugaba Biden. Shugabannin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi da musayar ra’ayi kan dangantakar kasashensu da batutuwan da ke jan hankulansu.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, ganawarsa da shugaba Biden a watan Nuwamban bara a birnin San Francisco, ya bude wata mahangar makomarsu. Ya ce cikin watannin da suka gabata, jami’an kasashen biyu sun aiwatar da matsayar da suka cimma sahihanci. Kuma dangantakar Sin da Amurka ta fara daidaituwa, sannan al’ummomin kasashen biyu da ma na kasa da kasa na maraba da hakan. Ya ce a daya bangaren, abubuwan dake yin mummunan tasiri kan dangantakarsu na karuwa, don haka akwai bukatar bangarorin biyu su mayar da hankali kan su.

Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, batun Taiwan shi ne iyaka ta farko da bai kamata a tsallake ba a dangantakar kasashen biyu. Ya ce kasar Sin ba za ta nade hannu tana kallon ayyukan ‘yan aware masu neman ‘yancin yankin da tallafi da goyon bayan da ake ba su daga waje ba.

A nasa bangaren, shugaba Biden ya ce dangatakar Sin da Amurka ita ce mafi tasiri a duniya. Kuma ci gaban dangantakar da aka samu bayan ganawarsu ta San Francisco, ya nuna cewa bangarorin biyu za su iya inganta hadin gwiwarsu tare da hakuri da bambance-bambancen dake akwai tsakaninsu.

Joe Biden ya kuma nanata cewa, Amurka ba ta neman tada sabon yakin cacar baka, kuma ba ta da muradin sauya tsarin kasar Sin, haka kuma kawancen da take yi ba ya nufin yi wa Sin taron dangi. Kazalika, Amurka ba ta goyon bayan ‘yancin yankin Taiwan, kuma ba ta neman tada rikici tsakaninta da Sin. Bugu da kari, ya ce Amurka tana goyon bayan manufar Sin daya tak a duniya. (Fa’iza Mustapha)