logo

HAUSA

Zimbabwe ta ayyana shiga yanayin ibtila’i sakamakon fari

2024-04-03 20:25:37 CMG Hausa

 

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya ayyana yanayin ibtila’i a kasar dake kudancin Afirka, sakamakon yanayin dumamar saman teku ko “El Nino”, wanda ya haifar mummunan fari a kasar.

Shugaba Mnangagwa, ya bayyana hakan ne a Larabar nan, cikin jawabin da ya yi wa ‘yan kasarsa daga fadar gwamnatin dake birnin Harare, inda ya ce, fari da kasar ke fama da shi, na barazana ga shirin samar da isasshen abinci a kasar.

Ya ce, an samu koma-baya game da hasashen yabanyar da za a samu yayin kakar noma ta shekarar 2023 zuwa 2024, saboda fari da yanayin “El Nino” ya haddasa. Sakamakon hakan, sama da kaso 80 bisa dari na kasar bai samu isasshen ruwan sama kamar yadda aka saba ba.

Shugaban na Zimbabwe ya kara da cewa, binciken farko-farko ya nuna Zimbabwe na bukatar kashe kudi sama da dalar Amurka biliyan 2, wajen aiwatar da matakai daban daban na shawo kan wannan matsala.  (Saminu Alhassan)