logo

HAUSA

Babban yankin kasar Sin na maida hankali sosai kan bala’in girgizar kasar da ya afkawa Taiwan

2024-04-03 11:27:19 CMG Hausa

Rahotannin sun ruwaito cewa, da misalin karfe 7 da minti 58 na safiyar yau Laraba 3 ga wata ne, aka samu iftila’in girgizar kasa mai karfin maki 7.3 da zurfin kilomita 12 a yankin teku dake gundumar Hualien ta lardin Taiwan na kasar Sin. Lamarin da ya haifar da girgiza mai karfi a wurare da dama na Taiwan, tare da hallaka mutane 4 da jikkatar wasu 97 a wurin.

Mai magana da yawun ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Zhu Fenglian ta bayyana cewa, babban yankin kasar na maida hankali matuka kan bala’in, da mika gaisuwa da fatan alheri ga ‘yan uwa dake Taiwan, kuma zai ci gaba da maida hankali kan bala’in gami da abubuwan da ka iya faruwa a nan gaba, da son samar da agaji don yaki da bala’in. (Murtala Zhang)